DAGA JAGORAN MPC
M.P.C (MOVEMENT FOR PROGRESSIVE CHANGE)
mal kabiru abubakar
Bayan nasarar da duniya take ganin kasar
Nigeria tayi wajen hambare gwamnatin kasar wadda ta sha soke-soke daga yan
adawa dangane da zargin nuna bangaranci a wajen raba albarkatun da allah ya
azurta kasar dashi atsakanin johohin kasar, dakuma yin ayyukan ci gaba ta
hanyar zabe abin kamantawa a idanun kasashe masu tasowa. Yayin da talakawan kasar
ke cike da zumudin samun tagomashin romon demokradiya dangane dayakini akan
ingancin abinda suka zaba saboda ingantaccen tarihin da ake ganin ‘yan takarkarun
sun kafa abaya. Da kuma kyakykyawan zaton cewa sunsan halin da kasar take ciki
kumasunsanhalin datalakawa suke ciki kuma, kuma sun san abinda talakawa suke
bukata. Har kawo yanzu da gwamnatin ta shiga shekara ta biyu a zangon mulkinta
talakawa basu daina zuba idon idanun ganin alamara sun sawya ga barin halin da
suke ba. Alumma basu samu kulawa ta bangaren tsadar abin bukata na yau da
kullum ba. ‘ya’yan talakawa basu sami yantuwa daga tsohuwar aladar ajiye
fursunonin dake jiran sharia agidajen yari ba tare da an kula da yi musu sharia
ba. Mun sami labarin wani yaro mai tabin hankali da yayi yunkurin gudu daga
babban gidan yarin kano . wani babban jami’i a gidan yasa aka kawo mai kulki ya
dinga maka masa har sai da yamutu. Mun zuba ido
muga abinda akayi akai. Ko kuma muci gaba dasanarwa duniya. Al’adar
alummar wannan kasar shine duk sanda shugaba yayi wani abu ba daidai ba sai a
mara masa baya musamman idan mutum yana cin moriyar gwamnatin saboda kada ludayinsa
ya sauka daga kan dawo. Wannan ba dabi’a
ce ta ci da kasa gaba ba. Dole mu koyi dawo da shugabanni hayyacin su ta hanyar
fadin abinda muka sani na hakikanin gaskiya. Ta hanyar lafuzza tausasa ba
harigido ba.
Yakamata shuwagabanni su cimma tabbatacciyar
matsaya wajen rattaba hannu akan hukunci mai tsanani ga duk shugaban da aka
same shi da wadaka da kudin al’umma. Banga dalilin da za’a saki manyan barayi
su dinga yawo acikin manyan motoci da gidaje su shiga kasashen da suka ga dama
da kudin alumma, a dinga tsare ‘ya’yan talakawa akan wata sata wadda bata taka
kara ta karyaba. Domin a zahiri su (manyan)sune suke wawashe lalitar kasar su kai kasashen duniya su adana, wanda hakan ya jawo takura da rashin walwala
ciki da kewayen kasar wanda hakan ya haifar da kananan sace-sace a tsakanin
matasan kasar. Wata rana a unguwarmu an taba kama wani yaro ya saci risho,garin
kwaki,da tukunya kai da ji kasan yunwace. Saboda ya wayigari babu wata dama
dazai alkinta kansa da ita data rage masa. Duk an wawashe anje an gina wasu
kasashen dasu. Dayawa akwai kasashenda ajiye-ajiyen da shuwagabannin mu suke
acikin bankunan su da kuma kamfanonin da suke zuwa su kafa acan shine abinda
yan kasar suke samun tattalin arzikinsu da shi. Wannan wane irin gwaranci ne,
ka kashe naka ka raya na wasu. Mun samu labarin wani shugaba daya tura wasu
kudi masu yawan gaske account din wani abokinsa dake ketare sai daya sauka yaje
a bashi kudin shi kuma abokin nasa yace bai san zancen ba. Kunga anyi biyu
babu. Ni a ra’ayi na idan har za’ayi maganin manyan sace-sace acikin gwamnati
to kai tsaye anyi maganin yawan sace-sace
acikin al’umma. Domin wancan shi ya haifar wannan. A karshe muna tabbatar wa da gwamnati
cewar mun san tana iya bakin kokarinta. Hakika muna amfani da wannan damar
wajen sanar da mutane cewar hakika gwamnati tana bakin kokarinta, musamman a
matakin tarayya. Mu kuma a matakai na jihohi dole ne mu cire tsoro mu haska mata
abubuwan dake faruwa domin ta sani ta maganta. kuma muna amfani da wannan dama
wajen haskawa yan siya sa cewar mu ba ‘yan adawa bane, bama adawa da kowacce gwamnati a siyasance. Mudai muna
sa ido ne a matakin addini da , sharia da zamani. Ban kafa wannan cibiya ta M.P.C
don yin adawa da gwamnati ko yiwa wani dan siyasa aiki ba. Muna yiwa
shuwagabanninmu fatan Allah yayi musu jagoranci, muna fatan Allah ya warware
dukkan matsatstsalun Nigeria , muna fatan Allah ya sanya wannan kasa tamu
acikin jerin manyan kasas shen duniya . Allah ya kunyata makiyanmu masu son
suga mun shiga cikin rudanin siyasa. wassalamu alaikum
Mal kabiru
abubakar
No comments:
Post a Comment