Saturday, November 13, 2010

A GANINA:

DALILIN DA YA SA BOKO YA TSERE WA AJAMI A HALIN YANZU
daga John E. Philips, Yabase, Akita, Jafan



--------------------------------------------------------------------------------

Ana buga littattafai da jaridun Hausa ta hanyoyin rubutu iri guda biyu.  Amma fa, hanyar boko ta rinjayi hanyar Ajami a halin yanzu.

Me ya sa haka?  Ko saboda boko na ilmin zamani ne?  Ko ko saboda wata babbar k'ullalliyar mishan ce?

Wannan babbar matsala ce a tarihin harshen Hausa.  Akwai maganganu daban daban a kan matsalar, amma saboda binciken da aka yi a gidan adana takardun tarihi a Kaduna, a jaridar nan da kake editan za ka ga labarin na hak'ik'a.

A lokacin da Turawa suka zo nan Nijeriya, Hausawa sun yi rubuce-rubuce a harshensu tun-tuni.  Wasu malami, musamman d'an Marina na Katsina, sun yi amfani da bak'ak'en Larabci don rubuta wak'ok'in Hausa har suka k'irk'ira wasu sababbin bak'ak'e, kamar su tsa, don rubutun Hausa daidai wa daida.

Kafin zuwan Turawa ana amfani da Larabci don aikin hukuma da yin wasik'a a k'asashen nan na Afirka ta yamma.  Hausawa fa, suna rubutun wak'ok'in da yarensu da hanyar Ajami.  Wasu 'yan mishan da masu ilmin harsuna, su kuma suna yin k'ok'arin su rubuta Hausa a boko.  Amma ba su daidaita ba a kan yadda za a rubuta sautin Hausa da bak'ak'en boko.

Duk da haka ko Hausawa ba su daidaita a kan yadda ba su rubuta sautin Hausa a  bak'ak'en Ajami ba.  Har yanzu ana rubuta tha' a Kananci, amma ana rubuta shin [mai d'igo a k'ark'ashi] a Sakkwatanci [don "c" a boko].

Ko a farkon k'arni na ashirin akwai 'yan mishan  wad'anda suka fi son rubutu da (Hausa) Ajami.  Misali Mallam Robinson, wanda ya wallafa k'amusi na Hausa da Turanci a lokacin su yana yabon ajami kuma ya buga wak'ok'in Ajami da sharhi a kansu a Ingila.

Da Gwamna Lugard ya ci k'asashen Hausawa da mak'wabtansu sai ya ba su sunan "Nijeriya ta Arewa".  Saboda k'a'idojin mulkin mallaka ya k'i ya bar Hausawa su ji abin da shi da wakilansa 'yan Ingila suke cewa a Turanci, kada su gane abin da Turawa suke nufi.  Kuma wani bature ya gano cewa dalilin da ya sa Magajin Keffi ya kashe ya kyaftin Moloney she ne saboda k'aryar da tafintar Moloney ya yi ne.

An yi bincike, an tabbata cewa ma fi yawan tafintoci ko dai su ne b'arayi ko suna cinikin bayi ko suna cin hanci.  'Yan Afirka wad'anda suka ci amanar 'yan Afirka ba su rik'on amanar Turawa.

To, shi ke nan, sai gwamna Lugard ya yi fushi da tafintoci, ya ba da oda cewa dole kowane bature wanda yake aikin gwamnatin Nijeriya ta Arewa ya koyi harshen Hausa.  Daga wannan oda ta shekara 1902 aka fara manufar nan "Ba Hausa, ba aiki."  a Nijeriya ta Arewa.  Wato in ba ka iya Hausa ba, ba za a ba ka aikin gwamnati ba.  An nad'a farfesan harshen Hausa a Jami'ar London don ya koya wa turawan Gwamnatin Nijeriya ta Arewa harshen Hausa.  Amma gwamnati ba ta yanke shawara cewa wace hanya za a bi a yi rubutun harshen Hausa don aikin gwamnati ba tukuna.

Akwai i Razdan a Sakkwato mai suna John Alder Burdon wanda ya goyi bayan Ajami.  Ya fad'a cewa tun da ba za a fitar da Ajami daga adabin Hauasa ba ya kamata a yi amfani da shi a aikin gwamnati, kada a sha wahala gina sababbin makarantun boko a ko'ina.

Ko d'an mishan d'in nan a Zariya mai suna Kokta Miller ya yi rubutu da Hausar Ajami.  Ya aika wa Gwamna Lugard da fassarar dokokin gwamnati a Ajami.  Miller da Robinson suna rik'a rubutun (Hausa) Ajami har wasu Turawan Gwamnati, misali Kyaftin Moloney, suna tsammani cewa Ajami ba rubutun Hausawa ba ne na 'yan mishan ne kad'ai.

Amma Gwamna Luard basi saurari wannan nasiha ba.  Gwamna Lugard ya k'i Ajami.  Ya tsaryar da shawara za a yi amfani da boko a aikin gwamnatin Nijeriya ta Arewa.

Wani d'an mishan mai suna Macintyre ya rud'i Gwamna Lugard.  Ya ga masa cewa Hausawa ba su iya karatun Larabci ba, har ya ce Ajami ba bak'ak'en Larabcin gaskiya ne ba.  Ya aika wa Gwamna Lugard da wasik'a a Larabcin Afirka ta Yamma, ya gaya masa cewa shi ne Ajami, kuma ya gaya masa cewa Ajami ba rubutun Hausa ta hanyar Larabci ba ne har Lugard yana tsammani Ajami wata hanyar rubutu ce dabam ke nan.  Macintyre ya gaya wa Lugard cewa Ajami hanyar rubutu wofaye ce domin babu azanci a ciki.  K'warai da gaske mutumin ya yi babbar k'arya, amma Gwamna Lugard bai sani ba.  Bai ji Hausa ba, balle Ajami ko Larabci.

Gwamna Lugard bai gane abubuwan da mutanen suka fad'a ba.  Shi bai fahimci bambanci tsakanin harshe da hanyar rubutunsa ba, har ya ce in ana amfani da boko, Turawa masu aikin gwamnati dole su koyi harshe guda d'aya, amma in ana amfani da Ajami, dole su koyi harshe guda biyu.  Duk da duhun kansa game da harsuna da hanyoyin rubutunsu, she ne Gwamna, she zai kafa odoji a Nijeriya ta Arewa.  Duk da yake shi masanin harshen Hausa ba ne, shi ya yanke shawara a kan hanyar rubutun Hausa.  Duk da shi ba malami ba ne, balle malamin ilmin koyarwa, shi ya ba da oda yadda za a rubuta harshen Hausa don aikin gwamnati da makarantun zamani a Nijeriya ta Arewa.

In an duba abubuwan da ya ajiye a fayil a Kaduna, tabbata cewa bai fahimci fa'idar amfanin Ajami ba.  K'warai da gaskiya bai fahimci hanyar rubuta Ajami ba, balle tarihinta.  Amma ya k'i bak'ak'en Larabci har ya auka wa k'asar Sudan da wasik'ar inda ya tambayi ko ana buga littattafan Larabci a boko.  Babu wata amsa daga Sudan a fayil a Kaduna.

Duk da haka, da Gwamna Lugard ya koma Ingila don hutunsa a shekarar 1903, sai walinsa William Wallace ya ba da oda a ranar 12 ga watan Satumba cewa dole a soma rubutun wasik'a a Hausa.  Babu masu ilmi boko a Nijeriya ta Arewa da yawa a lokacin.  Saboda odar, an daina karb'ar wasik'un Larabci a gidan Gwamna.  Wallace ya ce sai a fara karb'ar wasik'u a (Hausa) Ajami.

Da Gwamna Lugard ya komo sai ya sa Hans Vischer, watau d'an Hausa (wanda gidansa yake Kano har yanzu), ya koyar da Boko a wata makaranta a Birnin Kano.  Hausawa da dama sun shiga makarantarsa.  Suna so su fahimci ilmin zamani daga bakin bature.  Da suka gane ba za su koyi Turanci a makarantar ba, balle fasahar zamani sai da yawansu sai suka daina zuwa.  Don haka aka ce da makarantar "Makarkata."

K'warai da gaske an sha wahala, don ginin makarantun boko.  Saboda rashin yawan makarantun, ba yawan masu ilmin boko.  Sabo da rashin masu ilmin boko, ba masu aikin gwamnati sosai.  Saboda rashin ma'aikatan gwamnati, ba kud'in haraji sosai a Nijeriya ta Arewa, da Gwamna Lugard ya komo Nijeriya sai ya had'a Nijeriya ta Arewa dad ta Kudu a shekara 1914.

Ga mu nan sannu a hankali Nijeriya ta had'a kai, Hausar boko ta rinjayi  ta Ajami, amma a halin yanzu ba Hausa wadda take harshen gwamnati, sai Turanci.  Dalilin kuwa shi ne odar da Gwamna Lugard ya ba da.

No comments:

Post a Comment